By Ishaq Dabai
Hukumar kula da hana zagon ƙasa ta kama uwargidan Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Ganduje.
Wannan na ƙunshene a cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaru na jahar Malam Muhammad Garba ya fitar, inda yace labarin dake yawo, baza’a iya samun shi a duk wata kafa da take ingantacciya ba na cewa EFCC sun kama ta.
Yayi nuni dacewar abin baƙin cikine, yanda aka ƙirƙiri labarin ƙanzon kurege a kafafen sadarwa na zamani, ba tare da tabbatar wa daga Gwamnatin Jahar ko kuma EFCC.
Malam Garba yace ba’a kama matar Gwamnan ba, ko kuma tsare ta, domin a halin yanzu tana gudanar da harkokin ta.
Kwamishinan yayi kira ga al’ummar jihar Kano dasu jefar da wannan jita-jita, tare da kasancewa cikin kwanciyar hankali.
Comments 1