Rahotanni sun nuna cewa, wasu motoci da dama a ranar Laraba sun Kone gurmus a harabar wurin tashar mota ta 1 na sakatariyar gwamnatin tarayya, dake Abuja.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da ma’aikata ke shirin rufe Ofisoshin su domin tashi aiki.
Kazalika Wani rahoto da majiyar jaridar Dimokuradiyya ta samu ya ce, daga baya an tura jami’an kashe gobara domin kashe wutar.
Wani ma’aikacin gwamnati ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilin Jaridar Daily Trust.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda sun kama wata Mata da zargin Damfarar sama da Naira Milliyan 34 a Katsina
Inda ya ce “Wata Mota ce ta Sami matsala a fannin wuta, wanda haka ya haifar da gobarar kuma an kashe kafin ta yi muni.” inji shi.
Sai dai Kuma ya bayyana cewa, mota daya ce abin ya shafa.
A wani labarin Kuma na daban.
Gwamnatin jihar Gombe ta amince da sama da naira biliyan daya don biyan kudaden takwaran aikin UBEC, diyyar filaye da inganta asibitoci biyu.
Kwamishinan Yada Labarai da Al’adu na jihar Mista Julius Ishaya ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar.Ishaya yace an amince da jimlar kudi Naira miliyan 715 don biyan kashi 50 na kudin UBEC na shekarar 2021 don samun damar sauran kashi 50 na UBEC.
Hakanan an amince da jimlar Naira miliyan 117 don haɓaka asibitin Cottage da Cibiyar Kiwon Lafiya matakin Farko a Kuri dake ƙaramar hukumar Yamaltu da Deba.
Sannan Yace matakin inganta cibiyoyin kiwon lafiya guda biyu ya biyo bayan mummunan halin da suke ciki, a cewarsa, an sami barkewar cutar a mai da gudawa a yankin kuma cibiyoyin kiwon lafiya biyu sun wuce gona da iri, don haka akwai bukatar ingantasu
Alhaji Usman Jafun, Kwamishinan filaye da safiyo, yace majalisar ta amince da Naira miliyan 177 don biyan diyyar filayen da aka ware wa Jami’ar Tarayya Kashere (FUK) da kwakejin fasaha ta Kaltungo da kuma Golf Coursein Gombe.
Allah yayi jagora amin.