A halin yanzu kulle shafin Twitter ya shiga kwanaki 124, wanda yayi sanadiyyar rasa Naira Biliyan 309.26 ga tattalin arzikin Nigeria.
Gwamnatin Nigeria ta bada umarnin kulle shafin Twitter a ranar 4 ga watan yunin shekarar 2021.
A ƴan kwanakin nan, Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yace “Kafafen sadarwa na zamani, shafuka ne da suke taimakawa Miliyoyin ƴan Nigeria wajen ƙarfafa zumunci, da bunƙasa harkokin kasuwanci, da kuma samun bayanai.
“A kwanakin baya ya nuna cewa bawai ana amfani da Twitter domin tura labarai, amma wasu na amfani da shafin wajen shirya yadda zasu gudanar da ta’addanci, da tura labaran ƙanzon kurege, da kuma ƙarfafa rashin jituwa musamman a fagen ƙabilanci da addini.
“Domin magance wannan matsala ya sanya Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta dakatar da harkokin Twitter a ƙasar a ranar 5 ga watan yunin shekarar 2021, domin baiwa Gwamnati damar magance waɗannan matsaloli.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan sakai sun kashe wani Limami, da wasu mutum 10 a Jahar Sokoto
Acewar kafar NetBlocks, duk awa ɗaya yana janyo Najeriya asarar Miliyan 103.92 ($250,600) domin kulle ta, wanda a halin yanzu anyi awanni dubu 2,976, tun bayan kulle ta da akayi.
Gwamnatin Nigeria a lokutta da dama tana cewa ta kusa cire dakatarwa data yi.
A jawabinshi na ranar bikin murnar cika shekaru 61 da samun ƴancin kai, Shugaba Buhari yace baza’a cire wannan takunkumi ba, har sai sunyi rajista a Nigeria, kuma sai suna da wakilai.
A farkon shekarar nan, Twitter ta buɗe ofishin ta na Afirka a ƙasar Ghana. Kamfanin yace ya lura dacewa, Ghana tafi kayayyakin sadarwa da bada damar faɗin magana a yanar gizo da kuma inda ba yanar gizo ba