Jirgin da ya baro kasar Saudiyya dauke da Mahajjatan jihar Neja 550 sun isa filin jirgin sauka da tashi na Minna a Nijeriya. Umar Lapai, mukaddashin Sakataren hukumar lura da aikin hajji na jihar, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a garin Minna jim kadan da saukar mahajjatan da suka fito daga kananan hukumomin Edati, Mariga, Mashegu da Rijau.
Ya tabbatar da cewa; tawaga ta biyu ta mahajjatan za su baro birnin Jedda a ranar Laraba domin isowa Nijeriya. Mahajjatan wanda majiyarmu ta samu zantawa da su, sun ce sun kwashe awa 14 a Jeddah kafin a tantance su su baro can domin su iso Nijeriya.
Rahotanni sun tabbatar da cewa; akwai mahajjatan jihar Neja 3, 200 wadanda suka samu zuwa kasa mai tsarki domin halartar aikin Hajji na bana.