Jam’iyyar adawa ta PDP a ranar Laraba ta bukaci jam’iyyar APC Mai Mulki da ta amince da gazawarta a dimokradiyya kuma ta daina damun yan Nigeria da kukan ta na yau da kullun.
Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, ne ya mayar da martani kan kalaman APC inda ta yi ikirarin cewa, ta inganta tsarin zabe a kasar.
Ologbondiyan ya ce: “Abin da ya ke damun al’umar kasar nan shine, yadda APC ta lalata tattalin arzikin mu, tsarin zaben mu da hadin kan mu a kasar nan, har ta kai talakawan Nigeria sun yanke kauna daga Jam’iyar APC.”
Ya ce kamata ya yi APC ta fara shirya takardun Mika Mulki, saboda ‘yan Nigeria ba a shirye suke su jure wahalar da suke ciki ba.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutanen da suka kamu da Corona a Nigeria
Ya Kuma bukaci ‘yan Nigeria da su ci gaba da yin gangami tare da jam’iyyar, yayin da a shirye take ta kwato al’ummar kasar daga abin da ta kira “rashin cancanta, rarrabuwar kawuna da rashin tunani na APC, da gwamnatin ta.
Comments 1