Kotun koli a ranar Alhamis ta tabbatar da Farfesa Charles Soludo a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APGA a zaben Anambra da aka shirya gudanarwa ranar 6 ga Nuwamba, shekara 2021.
Kwamitin mutum biyar karkashin jagorancin Mai shari’a Mary Odili ya Kuma tabbatar da Mista Victor Oye a matsayin shugaban jam’iyyar.
Kotun kolin, ta shawara guda da kwamitin mutum biyar na alkalan karkashin jagorancin Mai Shari’a Mary Odili, inda Kuma ta tabbatar da hukuncin kotun daukaka kara ta jihar Kano, wacce ta tabbatar da zaben farko da ya ai’yana Soludo a matsayin Dan takarar Jam’iyar.
A cewar Kotun Kolin, kotun daukaka kara ta yi daidai lokacin da ta soke hukuncin Babbar Kotun Jihar Jigawa da ta amince da zaben fidda gwani da aka gudanar wanda bangaren Jude Okeke na APGA ke jagoranta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutum 3 na Makarantar Seminary dake Kaduna sun Shaki Iskar Yanci
Idan za a iya tuna Soludo ya fito zaben fidda gwani wanda babban jigon jam’iyyar ta APGA Victor Oye ke jagoranta ya shirya.
Comments 1