Wani mutum da ake kyautata zaton shekarunsa sun kai ashirin, a ranar Laraba a garin Ogidi na karamar hukumar Ilorin ta yamma, ya kashe kansa.
An tsinci gawar sa da aka daure a kan rufin wani gini da ba a kammala ba, yana rataye.
Mazauna yankin sun yanke igiyar da aka daure a wuyansa don saukar da gawar mamacin.
Kafin ya kashe kansa, marigayin ya cire tufafinsa, Wanda ya rage daga shi Sai dan kamfai.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta tabbatar da Soludo a Matsayin Dan Takarar Gwamnan a Jam’iyar APGA
Harkawo hada wannan rahoton ba a bayyana dalilin da ya sa matashin ya aikata hakan ba, Amma wata majiya ta ce, ya yi korafin shiga cikin mawuyacin hali kafin ya aikata laifin.
Yawancin mazauna yankin Ogidi, wadanda suka zanta da Jaridar Daily Trust sun bayyana kaduwarsu kan lamarin.
A cewar wani mazaunin garin, wanda kawai ya sanya sunansa a matsayin Taiye: “Alao ya yi korafin shiga cikin mawuyacin hali na wani lokaci yanzu. Amma ba mu taɓa sanin zai kai aikata irin wannan aikin ba.
“Abin mamaki ne a gare mu lokacin da muka ga gawar sa a rataye bayan wani daga cikin al’umma ya ja hankalin mu zuwa gare shi”, in ji shi.
Ya kara da cewa marigayi Mai suna Alao har yanzu bai yi aure ba, kuma ba shi da yaro ko daya.