Daga wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Fitaccen Furodusa wanda a yanzu ya fi kowa shirya fim a masana’antar finafinai ta Kannywood ya yi kira ga matan da su ke rububin shigowa harkar fim da su Dakata su je su nemi wata sana’ar ko su samu mijin aure. Furodusa ya bayyana cewa “Mata da yawa da su ke shigowa harkar fim su na shigowa ne ba tare da izinin iyayen su ba kuma daga baya idan suka yi suna a idon duniya kuma sai su zama fitsararru”.
Ya ci gaba cewar “ina amsa kiran waya a kalla sau 50 a rana guda ta matan da su ke son shigowa harkar fim, don haka ina kira a gare su da su koma makaranta su ci gaba da karatu ko su kama wata sana’ar, idan kuma hakan bai samu ba su samu miji su yi aure, domin kuwa muma matan da su ke cikin harkar a yanzu sun yi mana yawa, muna yi musu addu’ar Allah ya sa su samu mazajen aure. Don a yanzu matan da su ke cikin harkar sun yi waya sosai. “
Comments 1