Wasu daga cikin jami’an jihar da mambobin jam’iyyar PDP a Yobe sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, inji rahoton kamfanin dillancin labaran Nigeria NAN.
Wadanda suka koma APC sun hada da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na jiha, Alhaji Usman Amale, da Mataimakin Sakataren jam’iyar, Malam Ahmadu Biriri.
Gwamna Mai Mala Buni, wanda kuma shine Shugaban riko na Jam’iyar APC, ya gode musu saboda kasancewa cikin masu yunkurin “ceto Nigeria”.
“A yanzu jam’iyyar APC wani yunkuri ne da ke taimakawa kan hadin kai, ci gaban Al’uma da ci gaban Nigeria.
KARANTA WANNAN LABARIN:Kwalara ta kashe Akalla Mutane 23, yayin da 500 suka kamu a Adamawa
“Muna maraba da manyan ‘yan Nigeria daga kowane fanni na rayuwa, daga fannoni daban-daban, al’adu, addinai da yanayin siyasa.” Inji shi.
“Maganin matsalolin da Nigeria ke fuskanta ya ta’allaka ne da kwanciyar hankalin siyasar kasar; ya kamata dukkanmu mu taru don inganta hadin kanmu don ci gaban kasar ”in ji Mala Buni.
Kazalika ya tabbatar wa masu sauya shekar samun hakkokin su, kamar kowane memba don ba da gudummawa wajan a ci gaban Nigeria.
Da yake magana a madadin wadanda suka sauya shekar, tsohon mataimakin shugaban PDP, ya ce ba su da wani dalili da ya rage mu na zama a jam’iyar PDP, kuma ya nemi afuwar jinkirin da sukayi na rashin komawa APC akan lokaci.
A wani cigaban Kuma duk dai a jihar ta Yobe.
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da sake fasalin shekarun ritaya na malamai daga shekara 60 zuwa 65.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar (HoS), Alhaji Muhammad Nura, inda ya bayyana hakan a Damaturu ranar Talata.
Nura yace an kuma duba shekarun ma’aikatan gwamnati daga shekaru 35 zuwa 40.
“Wannan karimcin ya takaita ga jami’an ilimi da ma’aikatan koyarwa kawai, kuma sanarwar ta fara aiki nan take,” in ji Nura.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Nura yace duk da haka, shekarun da ake yin ritaya da shekarun aiki bana kai tsaye bane saboda za a buƙaci jami’ai su nuna ƙoshin lafiya bayan an duba lafiyarsu.in jishi