By Ishaq Dabai
Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya amince da sake fasalin shekarun ritaya na malamai daga shekara 60 zuwa 65.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan jihar (HoS), Alhaji Muhammad Nura, inda ya bayyana hakan a Damaturu ranar Talata.
Nura yace an kuma duba shekarun ma’aikatan gwamnati daga shekaru 35 zuwa 40.
“Wannan karimcin ya takaita ga jami’an ilimi da ma’aikatan koyarwa kawai, kuma sanarwar ta fara aiki nan take,” in ji Nura.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Nura yace duk da haka, shekarun da ake yin ritaya da shekarun aiki bana kai tsaye bane saboda za a buƙaci jami’ai su nuna ƙoshin lafiya bayan an duba lafiyarsu.in jishi
Comments 1