By Ishaq Dabai
Wata gidauniya mai zaman kanta, ta raba kudi Naira miliyan 11.6 a matsayin tallafin karatu ga dalibai 116 dake karatu a jami’ar Ahmadu Bello Zariya da Jami’ar Jihar Kaduna.
A cewar gidauniyar, an yi hakan ne da nufin bunkasa bangaren ilimi ta hanyar tallafa wa gwamnati da kwararrun malamai tare da rage jahilci a cikin al’umma.
Shugaban mai sanya ido na shiyyar jihar Kaduna, Malam Muhammad Danfulani, yace a yayin taron kwana daya na gidauniyar tana da ayyukan agaji a fannonin ilimi, ruwa, lafiya da kuma yunwa.
“A karkashin ayyukan agaji na ilimi, gidauniyar tana bada tallafin karatu ga ɗalibai, tana bada fakitin kayan rubutu ga makarantu kuma tana tallafawa sabunta makarantun marayu,” in ji shi.
Daga cikin ɗalibai 116, jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa 101 ɗaliban ABU ne da mata 40 da ɗalibai maza 61 yayin da ragowar 15 ɗaliban jami’ar KASU ne. Kowanne daga cikin masu cin gajiyar zai karɓi alawus na naira 10,000 na tsawon wata 10.
Ya kara da cewa gidauniyar ta kuma dauki nauyin dalibai 40 zuwa cibiyar jarabawar shiga makarantu masu zaman kansu dake Kaduna inda ta kashe kudi naira miliyan 2.4 kan horon don baiwa daliban damar samun shiga jami’o’i.
Kazalika yace gidauniyar tana kuma tallafa wa ɗalibai 200 da kudi naira 40,000 kowannensu don rubuta jarrabawar Babbar Makarantar daga Hukumar Kula da Jarabawar Ƙasa (NECO) tare da Jarrabawar Yammacin Afirka (WAEC).
Dakta Adamu Abubakar-Sadeeq, malami a Sashen Koyar da Dan Adam, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, ya roki gidauniyar data fadada yawan malanta don samun ƙarin ɗalibai a cikin shirin.
Mista Behlul-Fatih Basaran, wanda shine shugaban, gidauniyar yace gidauniyar ta bayar da tallafin karatu ga dalibai 521 a jami’o’i a duk fadin kasar.
Comments 1