Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci bude taron wayar da kai kan da’ar aiki da bayyana kadarori na yini biyu.
Conde of Conduct Bureau da hadin gwiwar ma’aikatar kananan hukumomin jihar Kano suka shirya karkashin Jagorancin kwaminan ma’aikatar, Hon. Murtala Sule Garo.
Taron wanda aka shiryawa Shugabannin Kananan Hukumomi da Kansiloli zababbu da nadaddu da sauran ma’aikatan ma’aikatar kananan hukumomin, an gudanar dashi ne a dakin taro na meena dake Lodge Road a cikin Garin Kano.
Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamna, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Sakataren Gwamnati Alhaji Usman Alhaji da shugaban jam’iyyar APC, Alhaji Abdullahi Abbas da wasu Kwamishinoni, da kuma sauran jami’an Gwamnati.
A wani labarin Kuma makamancin wannan.
Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci kaddamarwa tare da mika takardun kama aiki ga wakilan Hukumar gudanarwa da harkokin Majalisar Dokoki ta jiha.
Gwamnan Ganduje ya kaddamar da Hukumar ne yayin zaman majalisar Zartarwa na mako-mako na musamman tare da Maitamakin sa, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da Sauran kwamishinoni da yan majalisar zartawa, wanda aka gudanar a dakin taro na Africa House dake Gidan Gwamnati.
Gwamnan yace yana da kwarin gwiwar cewar wakilan Hukumar za su yi aikin su yadda yakamata ta yadda majalisar za ta gudanar da ayyukan ta yadda yakamata wajen gudanar da harkokin ta na yau da kullum.
Hukumar na karkashin Shugancin Alhaji Nasiru Mu’azu Kiru da mataimakin sa Hon. Ishaq Tanko Gambaga da sauran mambobi Takwas.
Ka’ida na wa’adin Shugabancin Hukumar da wikilan ta shine shekara hudu.
Comments 1