Hukumar Kula da Jiragen Ƙasa ta Nigeria ta tsaida zirga-zirgar jirgin ƙasa daga Abuja zuwa Kaduna, inda ta tabbatar da cewa wani yanki na jirgin a Rijana da Dutse an farmake shi da manyan makamai a Jahar Kaduna a ranar Laraba.
Babban Daraktan Hukumar Fidet Okhiria wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace daga ranar Alhamis, dole za’a tsaida zirga-zirgar jiragen domin gudanar da ƙwaƙƙwaran bincike akan lamarin.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya Shehu Sani ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa ƴan ta’adda sun farmaki jirgin daya shigo daga Abuja zuwa Kaduna a ranar Laraba, da bama-bamai, da kuma buɗe wuta, inda suke son harbin direba da tankin man jirgin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya karɓi rahoton yanayin tsaro daga Hafsoshin Tsaron Ƙasa
Dayake maida jawabi akan lamarin Okhiria ya shaidawa majiyar jaridar Dimokuraɗiyyar cewa, akwai inda aka farmaki jirgin da bama-bamai, wanda ya sanya dole hukumar ta tsaida aikace-aikacen ta.
Yace “duk da an farmaki jirgin da manyan makamai, amma bazamu iya tabbatar wa cewa bom ne ba.
“An tsaida zirga-zirgar jirgin daga yau domin bincike, kuma muna fatan kafin kammala bincike zuwa wani lokaci munyi abinda ya kamata.
Shugaban Hukumar ya ƙara dacewa “babu inda ƴan bindiga suka harbi jirgin, kuma ana bakin ƙoƙari domin cigaba da gudanar da harkokin jiragen.
Comments 1