By Abbas Yakubu Yaura
Mai ba da shawara na musamman kan hulda da jama’a, kafofin yada labarai da dabaru ga gwamnan jihar Borno, Isa Gusau, yace gwamnati zata rufe sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar saboda karuwar korafe -korafe na fyade da sauran ayyukan laifi.
Gusau, wanda ya yi magana a wata hira da wakilinmu, yace, “Ana samun karuwar yawan fyade tsakanin matasa a cikin ‘yan gudun hijira. Hakanan akwai batutuwan kwayoyi da laifuka da yawa da ayyukan rashin da’a dake gudana a cikin waɗannan sansanonin.
“Gwamnatin jihar, bayan ta duba irin hatsarin da ke tattare da illolin wadannan munanan ayyuka, ta yanke shawarar rufe irin wadannan sansanonin.wadanda aka yisu don kyautatawa ‘yan gudun hijira da sauran jama’a.“Abu daya da ya tabbata shi ne cewa za a sake tsugunar da duk mutanen da suka rasa muhallansu a wasu wurare da Gwamnati ta gina gidaje don sake tsugunar dasu.
“Duk da cewa ba a sake ginawa dukkan al’ummomin da aka lalatawa muhallai ba, akwai sabbin matsugunan da ‘yan gudun hijirar za su yanke shawara daga inda suke son a sake tsugunar da su.”
Wata majiya a yankin na Borno wacce ba a ba ta damar yin magana da manema labarai ta ce, “Akwai sansanonin ‘yan gudun hijira na hukuma guda 28 da suke a cikin jihar yayin da daruruwan sansanonin al’umma da ke karbar bakuncin har yanzu suna da yawa.”
Sai dai kuma jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Wasu daga cikin mutanen da suka rasa muhallansu sun nuna fargaba kan sanarwar gwamnan jihar cewa za a rufe dukkan sansanonin ‘yan gudun Hijira, IDP da ke jihar kafin ranar 31 ga Disamba.