Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati ta tsare tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Anyim Pius Anyim, dangane da binciken da ake yi kan tsohuwar Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sanata Stella Oduah.
An gano dai cewa hukumar ta tasa keyar Anyim, a jiya Lahadi, inda ta tsare shi na awanni da dama dangane da wani asusun wanda aka gano wani kamfani da ya taba kasance darakta a Ma’aikatar.
An rahoto cewa ya isa ofishin EFCC da ranar Lahadi, kuma an yi masa tambayoyi sama da awanni shida.
Harkawo hada wannan rahoton bayanai sun nuna ce Anyim na tsare a tundaga jiya Lahadi, har zuwa hada wanann rahoton a yau Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi Gawon Gaba da Masu Ibada a Jihar Ogun
Tsare tsohon SGF na zuwa kwanaki kadan bayan an ambaci sunan Oduah a cikin takardun Rahoton “Pandora Papers” a matsayin daya daga cikin ‘yan Nigeria 10 da ke boye dukiyarsu a wuraren da ake biyan haraji.
An yi imanin EFCC ta fara binciken Oduah da wasu da aka ambata a cikin rahoton.
Wata majiya ta ce, “Gayyatar Anyim da tambayoyi na da nasaba da shari’ar safarar kudi da ta shafi tsohuwar Ministan Sufurin Jiragen Sama kuma Sanata Stella Oduah.
”Bincike ya nuna cewa, wani bangare na Kudaden ma’aikatar sufurin jiragen sama sun bace bat, inda aka Gano naira miliyan 780 a cikin kamfanin da Anyim ya taba jagoranta. ”
Daraktan yada Labarai da na EFCC, Mista Wilson Uwujaren ya ce, ba shi da wani bayani kan tsare Anyim.