By Abbas Yakubu Yaura
Hambararren Firaministan kasar Sudan Abdalla Hamdok yace a maido da gwamnatinsa da aka rusa ta hanyar juyin mulkin soji, zai iya samar da mafita a kasar.
A cewar ma’aikatar yada labaran, Abdella Hamdok ya yi magana ne a wata ganawa da ya yi da jakadun Amurka da Birtaniya da kuma Norway a gidansa inda ake tsare da shi.
Kafin haka dai, dubban ‘yan kasar Sudan sun fito kan tutuna don gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yunkurin kwace madafun iko da sojojin kasar suka yi a ranar 25 ga watan Oktoba, inda babban hafsan sojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan ya rusa gwamnatin kasar, ya kuma kafa dokar ta baci da kuma tsare shugabannin farar hula na Sudan.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Manyan biranen kasar da alama sun mutu tun bayan fara gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da hambarar da gwamnatin Abdalla Hamdok, Wasu nau’ikan ayyukan tattalin arziki sun tsaya cik.a Khartoum inda yawancin ma’aikatan gwamnati ke kin fita aiki a matsayin wani bangare na gangamin zanga-zanga a fadin kasar, Shaguna kadan ne aka bude.
An ga sojoji daga cikin sojojin kasar da kuma dakarun gaggawa a kan titunan Khartoum da Omdurman.