By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga sun hallaka ‘yan sanda bakwai a hanyar Tofa-Magami a karamar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Wani dan yankin mai suna Salisu Sani ya shaidawa jaridar PUNCH cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Litinin lokacin da jami’an ‘yan sanda suka je yankin domin yin sintiri.
Sani yace ” ‘yan bindigar sun yi wa jami’an ‘yan sanda kwanton bauna, inda suka kashe bakwai daga cikinsu tare da kona motar da suke aiki da ita.
Sani ya ci gaba da cewa ‘yan bindigar sun yi artabu da jami’an ‘yan sandan, inda a sakamakon haka ne aka kashe bakwai daga cikin ‘yan sandan.sannan yace “Naga an kai gawarwakinsu Gusau (babban birnin jihar),” in ji Sani.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kakakin asibitin kwararru na Yarima Bakura Gusau, Awwal Ruwan-Doruwa, ya tabbatar da cewa an kawo gawarwakin ‘yan sandan da aka kashe bakwai zuwa asibitin.
Sai dai kuma munyi kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu amma hakan mu bai cimma ruwa ba.