By Abbas Yakubu Yaura
Akalla mutane 15,000 ne aka kama da yin magudin jarabawar neman ilimi ta shekarar 2021 a jihar Bauchi.
Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi Aliyu Tilde ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai daya gudanar a ranar Laraba.
Yace dalibai 52,000 ne suka zauna yin jarawabawar BECE na bana tare da 45,000 daga cikin su daga makarantun gwamnati, inda yace daga cikin wannan akwai 15,000 da suka samu matsalar satar amsa da kuma rashin yin jarrabawa a bangaren rubutun.
Tilde yace “Ina da shaidar bidiyon dake nuna yadda suke satar amsar jarabawa a hannuna. Ba za mu azabtar da daliban ba amma tabbas zamu hukunta manyan jami’ai. Kuma ba zai basu damar gudanar da jarrabawa na gaba ba. Wannan shi ne mafi ƙarancin da zamu iya yi kuma za muyi hakan. “
Sannan yace jarrabawar filesiman ga dalibai ya zama dole, ya kara da cewa, “kusan kashi daya bisa uku na daliban da suka samu rahoton jarrabawar shaidar kammala karatu a makarantu ne.”
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kwamishinan yace an fara jarrabawar ne tun ranar Litinin 8 ga watan Nuwamba, kuma za a kammala a ranar 15 ga watan Nuwamba, inda yace jarrabawar za ta sa su sami damar shiga makarantun JSS1, JSS2 l, SS1 da SS2.