By Abbas Yakubu Yaura
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi maraba da sanarwar cewa, kasashen Sin wato chana da Amurka sun amince su kara yin hadin gwiwa sosai kan ayyukan sauyin yanayi, yana mai cewa muhimmin mataki ne da yake kan hanyar data dace.
Labarin sanarwar hadin gwiwa tsakanin manyan kasashen biyu masu fitar da iskar gas, yazo ne a ranar Laraba a taron sauyin yanayi na shekarar 2021,na COP26 a Glasgow da kasar Scotland.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Idan za’a iya tunawa a birnin Paris a shekarar 2015, shugabannin sun yi alkawarin kokarin kiyaye duniya daga dumamar yanayi fiye da tsakanin 1.5C zuwa 2C ta hanyar rage hayakin da ake fitarwa.
A cikin sakonsa na twitter, Guterres ya yi maraba da yarjejeniyar da China da Amurka suka yi domin yin aiki tare don ɗaukar matakai masu ban sha’awa a cikin wannan shekaru goma, kuma ya lura cewa rikicin yana buƙatar haɗin gwiwa da haɗin kai na kasa da kasa.
Bayan sanarwar ba-zata, ta manyan jakadun yanayi na kasashen biyu sun gudanar da taron manema labarai na baya-bayan nan a COP26.
“Akwai ƙarin yarjejeniya tsakanin Amurka inji Xie Zhenhua, wakilin kasar Sin kan sauyin yanayi, yace, kasar Sin fiye da rarrabuwar kawuna, wanda hakan yasa ta zama wani yanki mai karfin hadin gwiwa.
“Ta hanyar yin aiki tare da kasashenmu biyu za su iya cimma wasu muhimman abubuwa da suke da amfani ba ga kasashenmu biyu kadai ba har ma da duniya baki daya.”
Kazalika kasar Amurka wanda Jakadan ta na musamman kan harkokin yanayi John Kerry, yace ya yi farin ciki da yarjejeniyar da kasashen biyu suka cimma, ya kuma ya kara da cewa: “Kowane mataki yana da muhimmanci a yanzu, kuma muna da doguwar tafiya a gabanmu.”