Yayin da kananan hukumomin Kibiya, Garko da Ajingi na jihar Kano suka samu matsayi na daya da na biyu da kuma na uku a gasar noma ta kasa da aka kammala kwanan nan a garin Karu na jihar Nassarawa, kwamishinan kananan hukumomi da al’amuran masarautu Murtala Sule Garo, ya gabatar da lambobin yabo guda uku ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
An gabatar da kyautukan ga gwamna ne a yayin taron majalisar zartarwa ta jiha, wanda ya gudana a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnati, a jiya Laraba.
A cikin dukkanin kananan hukumomi 774 na jihohi 36 na kasar nan, ciki har da babban birnin tarayya Abuja, Kano ta samu matsayi na daya da na biyu da na uku.
Garo ya ce makasudin shirya wannan gasar, shine “domin nuna karfin jihohi daban-daban a fadin kasar. Ta hanyar baje kolin amfanin gona da kayayyakin noma.
Gwamna Ganduje ya yabawa kananan hukumomin bisa yadda suka nuna kwarewa da jajircewa wajen lashe irin wannan lambar yabo.
Ya yi alkawarin ci gaba da tallafawa bangaren noma da dukkan jajircewa da azama.