Shugaban Hukumar kula da Samar da Magunguna ta Jihar Kano, Pharmacist Hisham Imamuddeen ya karbi bakuncin jami’ai daga ma’aikatar lafiya ta Jihar Sakkwato a rangadin binciken da suka kai ga hukumar a jiya Laraba.
Tawagar da ta kai ziyarar, ta kunshi manyan jami’an gudanarwa na ma’aikatar wanda ke karkashin jagorancin Pharmacist Murtala, da hukumar kula da magunguna ta jihar Sokoto da sauran su.
Pharm Hisham Imamudeen, a yayin da yake yi musu jawabi, ya bayyana musu wasu daga cikin ayyukan hukumar da kuma nasarorin da hukumar ta samu a baya-bayan nan, tare da yaba wa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yake bayar da goyon baya a fannin lafiya.
Ya kuma bayyana matukar jin dadinsa da matukar godiya ga Gwamna bisa yadda ya ware kaso mai tsoka ga fannin lafiya a cikin kudirin kasafin kudin shekarar 2022 da kuma tallafawa hanyoyin samar da kayayyaki duk da nufin inganta rayuwar al’ummar jihar.
Tun da farko a cikin jawabin nasa, Shugaban Kungiyar, Pharm. Murtala ya ce sun zo Kano ne domin wani rangadi ne da kuma koyan ayyukan hukumar domin inganta nasu.
Daga nan sai Pharm Murtala ya bayyana jin dadinsa da abin da suka gani, don haka ya yaba da iyawa da kuma sada zumuncin da shugaban ya yi domin ya yi alkawarin yin koyi da tsarin jihar Kano wajen inganta harkar samar da kayayyakin lafiya a jiharsu.