Rahotanni sun tabbatar da cewa wata Gobara ta tashi a kasuwar Gashuwa dake a jihar Yobe.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, ta bayyana cewa gobarar ta kone shaguna 20 baya ga gonaki.
Har ila yau hukumar ta jajantawa wadanda gobarar Kasuwar Gashua Zangon Kanwa ta shafa.
Lamarin da ya faru a daren ranar 11 ga watan Nuwamba 2021 kamar yadda masu bayar da agajin gaggawa na yankin suka ruwaito, kuma ya shafi manya-manyan rumfuna ke dauke da sinadarin Potash iri daban-daban.
Masu ba da Agajin Gaggawa na SEMA za su gudanar da tantancewa tare da ba da shawarar yiwuwar matakai don kawo taimako ga waɗanda abin ya shafa.
Har yanzu dai hukumar ma cigaba da tattara sakamakon asarar da akai a wannan gobarar, kumà da zarar sun kammala zasu sanar da manema labarai.