An harbe wani Birgediya-Janar a wani harin kwantan bauna da mayakan kungiyar ISWAP suka Kai wa rundunar soji a jihar Borno.
Rahotanni sun ce an kashe wasu sojoji hudu a lamarin wanda ya faru a Bulguma mai tazarar kilomita kadan daga garin Askira a karamar hukumar Askira Uba.
An ruwaito cewa dakarun ta 28 Task Force Brigade dake aiki a garin Chibok, sun hada kai domin ba da taimako a Askira, da aka kai wa hari tun da fari.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito yadda mayakan ISWAP suka kutsa cikin garin a cikin manyan ayarin motocin yaki.
Wani Mazaunin yankin ya ce sun kutsa kai cikin sansanin sojin ne, inda suka yi ta harbin bindiga ba kakkautawa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sojoji Sun Ragargaji Yan bindiga a Benue
An yi wa sojojin kwanton bauna ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta bayar da tallafi ga sojojin da ke fafatawa da ‘yan ta’addar.
“Rana ce ta bakin ciki a gare mu a lamari na yaki; mun rasa Birgediya Kwamanda (an sakaye sunan sa). Tare da wasu sojoji da ke kan hanyar zuwa tallafa wa sojojin mu a Askira, mayakan ISWAP sun yi musu kwanton bauna har lahira. Muna bakin ciki,” in ji wata majiyar tsaro.
Majiyar ta kara da cewa jiragen yakin sun yi ruwan bama-bamai kan kungiyoyin, amma ba a samu cikakken bayani ba.
Harin dai ya faru ne sa’o’i bayan mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Maj.-Gen. Babagana Monguno (Mai ritaya) ya ce, hadewar kungiyar ta’addanci ta Boko Haram da ISWAP yana shafar yaki da ta’addanci.