A ranar Asabar din da ta gabata ne mutane biyu suka mutu yayin da wasu 15 suka samu raunuka bayan da wata mota kirar DAF da ke gudun wuce sa’a, inda ta kife a wata karkatacciya da ke kan hanyar Legas zuwa Ibadan.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya tattaro cewa motar mai lamba RBH 214 XA dauke da buhunan albasa da fasinja, tana kan hanyar zuwa Legas ne a lokacin da hatsarin ya afku a kewayen Eldorado a kan titin.
Hadarin da ya afku da misalin karfe 6:30 na safe ya kai ga kulle, yayin da motar ta kwashe albasa da fasinjojin dake kan hanyar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar hatsarin a Abeokuta.
Ya jajantawa iyalan wadanda suka rasu, ya kuma gargadi direbobin da su rage gudun wuce kima yayin da suke kan hanya.