By Abbas Yakubu Yaura
Ministar kudi, Hajiya Zainab Ahmed ta alakanta tashin farashin shinkafa a Najeriya da cewar ayyukan masu fasa kwauri ne ya haifar da matsalar a cikin kasar.
Da take jawabi a wata hira, ministar ta bayyana cewa ayyukan fasa-kwauri na yin illa ga tattalin arziki da walwalar ‘yan Najeriya, lamarin da ta bayyana a matsayin abin takaici musamman ganin yadda wasu miyagun ‘yan Najeriya ke ci gaba da safarar kayayyakin da gwamnati ta haramta shigo dasu daga kasashen waje.
A cewar Ministan, akwai wasu ‘yan Najeriya marasa kishin kasa dake shigo da shinkafar da bata da inganci a cikin kasar, wasu kuma ba a cin abincin, inda tace a cikin samun karin riba ne irin wadannan ‘yan Najeriya ke safarar irin wannan shinkafar suna yadawa a kasuwanni. .
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Hajiya Zainab ta nanata kokarin gwamnati na dakile ayyukan masu fasa kwauri, inda ta yi nuni da cewa hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya, ‘yan sanda, da hukumar DSS da sauran su, dasu hada kai wajen ci gaba da dakile ayyukan haramun na masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.
Dangane da bukatar karin lamuni da majalisar ta baiwa gwamnatin tarayya dama, Zainab tace gwamnati ta samar da tsarin kula da basussukan na wani dan lokaci, tace ba ta hanyar kotu ba, wato fiat. ta inda gwamnati ke karbar lamuni.
Sai dai ta bayyana cewa neman rancen ba sabon abu ba ne domin gwamnati ta gabatar da bukatar lamunin tun farkon shekarar 2021, wanda aka amince da shi.
Comments 1