Kimanin mazauna jihar Nasarawa 51,000 da suka hada da marayu da almajirai da kuma tsofaffi ne aka yiwa rajista a tsarin inshorar lafiya na jihar.
Babban Sakataren Hukumar Inshorar Lafiya ta Jihar Nasarawa, Dakta Gaza Gwamna, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirye-shiryen hukumar a Lafia, babban birnin jihar.
Inda Ya bayyana cewa mabukata 51,000 da suka yi rajista don cin gajiyar shirin gwamnatin jihar Nasarawa, da wasu kungiyoyi masu zaman kansu ne suka dauki nauyin wannan shirin.
Ya ce: “Mun shigar da dukkan gidajen marayu da ke Jihar Nasarawa. Suna cikin shirin inshorar lafiya wanda gwamnatin jihar ta dauki nauyinsa saboda kyakkyawar zuciyar gwamna Abdullahi Sule.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Jihar Kano zata Inganta Alaka da Masar
“Mun kuma sanya yaran almajirai a jihar. Ya zuwa yau, mun yi rajistar mutane kusan 51,000 amma ba dukkansu ba ne aka biya su kudinsu. Muna da wasu daga cikinsu da gwamnatin tarayya ta biya su kudadensu, yayin da wasu kuma gwamnatin jihar da wasu kungiyoyi masu zaman kansu suka biya nasu.”
Gwamna ya yabawa kungiyoyin jihar kan yadda suka shiga shirin, inda ya ce, da zarar an cire su daga albashin ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho domin su dauki nauyin shirin, za su fara samun ayyukan kula da lafiya a karkashin hukumar.”
Wakilin majiyar Jaridar Dimokuradiyya ya ruwaito cewa, a kwanan baya kungiyoyin kwadago a jihar sun amince cewa za a fara cire kashi 3% na albashin ma’aikata a kowane wata da kashi 1% na ‘yan fansho ba tare da bata lokaci ba, sannan a mika wa hukumar domin baiwa wadannan nau’ukan mutane damar samun lafiya karkashin tsarin inshorar lafiya na jiha