Hukumar yaki da cin hanci da aikata rashawa ta (ICPC) ta shiga cikin wata badakalar takardar shedar bogi da badakalar shekaru, wanda ya shafi ma’aikata da dama, a cikin hukumar kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya tabbatar.
Da dama daga cikin manyan ma’aikatan da aka samu da hannu a wannan haramtacciyar hanya, an gano cewa ana shirin shirya wani gagarumin shiri daga hukumar da kuma bangaren gudanarwar hukumar yaki da cin hanci da rashawa domin yin saukale ga wadanda aka samu da laifi.
Ya zuwa yanzu akalla ma’aikatan hukumar 50 ne suka bayyana a gaban karamin kwamitin hukumar kan tantance satifiket din ma’aikata da bayanan hidima inda aka gano wasu kura-kurai a shekarunsu da kuma takardunsu.
A karshe dai shine ganin irin hukuncin da hukumar za ta zartar akan wadannan ma’aikata na ta.