By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, Echeng Eworo, ya umarci otal-otal dake fadin jihar dasu gaggauta mika jerin sunayen bakinsu a kullum ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa dasu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Ikenga Tochukwu, ya fitar a Awka dake babban birnin jihar a ranar Lahadi.
Sanarwar ta kuma bukaci asibitoci masu zaman kansu dana gwamnati a jihar dasu gaggauta kai rahoton duk wanda suka gani yana dauke da raunin harsashi ko kuma wani rauni daya samu a cibiyoyinsu ga ‘yan sanda.
Jami’in hulda da jama’ar yace daukar matakan wani bangare ne na kokarin dakile kalubalen tsaro da inganta tsaron jama’a da zaman lafiya a jihar a lokacin Yuletide.
Sanarwar tace , “Ana shawartar iyaye masu kula dasu mai da hankali sosai kan ayyukan ’ya’yansu da kuma gundumomin yankin su.
Kazalika“Su yi kokarin kai duk wanda ake zargi tare da kama shi zuwa ofishin ‘yan sanda mafi kusa, domin hakan zai baiwa ‘yan sanda damar gudanar da binciken daya dace da kuma gurfanar dasu a gaban kotu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa dokar da gwamnatin jihar ta yi na hana gurbatattun ababen hawa da lambobin da aka rufe har yanzu dokar tana ci gaba da aiki.
Sannan ya bukaci jama’a dasu kai rahoton duk wani cin zarafi da ‘yan sanda suka yi ta hanyar kiran layukan wayar da rundunar take dasu.