By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban makarantar Grammar Community ta Auga, Mista Joshua Adeyemi da mataimakinsa, Mista Ifedayo Yesufu da wasu malaman NPower guda uku.
An yi garkuwa da mutanen ne a hanyar Auga-Ise a lokacin da suke tsaka tafiya a cikin wata mota kirar Toyota Corolla a ranar Alhamis.
Lamarin dai ya rutsa da wata malama mai ciki a cikinsu mai suna Misis Blessing Okeke, an ce wadanda suka yi garkuwa dasu sun sako ta.
Misis Okeke tace wadanda suka sace su sun sha duka a lokacin da sukayi tattaki a cikin daji na sama da sa’a daya.
Wani jami’in dan sanda a sashin Ikare, wanda ya nemi a sakaya sunansa, yace an fara gudanar da aikin ceto kan lamarin.sannan ya ce an dauke motar da wadanda abin ya shafa ke tafiya daga inda aka bar ta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Lamarin satar mutane na karuwa tun lokacin da aka janye sojoji daga shingayen binciken ababen hawa a fadin jihar.Makonni biyu da suka gabata, masu garkuwa da mutane sanye da kayan sojoji sun yi awon gaba da wasu mutane da sunan kai su barikin sojoji.
An kai wadanda abin ya shafa zuwa jihar Kwara inda aka karbi kudin fansar sakinsu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ondo, DSP Fumilayo Odunlami, bai amsa kiran da mukayi masa ba har zuwa lokacin kammala wannan labarin.
Comments 1