By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa wani mutum mai shekaru 40, Richard Madubiko, a ranar Litinin ya bayyana a gaban wata kotun Majistare ta Ojo dake jihar Legas, bisa zargin sa da barazana ga rayuwar wani Mista Nnamdi Nwafor.
An gurfanar da wanda ake tuhuma kan tuhume-tuhume uku da suka hada da kai hari, rashin zaman lafiya da barazana ga rayuwa.
Sai dai wanda ake tuhuma ya musanta zargin aikata laifin.
Dan sanda mai shigar da kara, ASP Simeon Uche, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 10 ga watan Nuwamba a wani wuri mai suna BG House, kusa da madakatar motoci ta Sunny dake Ojo.
Yace biyo bayan rashin fahimtar juna da aka samu tsakanin wanda ake kara da wanda ya shigar da kara, wanda ake kara ya hana mai shigar da kara ba bisa ka’ida ba.
Mai gabatar da kara ya ci gaba da cewa wanda ake tuhumar ya kuma ci zarafin wanda ya shigar da karar ta hanyar ja shi a kan babur tare da yi masa barazanar kashe shi.
A cewar mai gabatar da kara, cin zarafi, rashin zaman lafiya da barazana ga rayuwa sun saba wa tanadin sashe na 56, 168, da 172 na dokar aikata laifuka ta jihar Legas ta shekarar 2015.
Kotun ta bayar da belin wanda ake kara a kan kudi Naira 100,000 tare da mutane biyu wadanda zasu tsaya masa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa alkalin kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar 21 ga watan Disamba