By Abbas Yakubu Yaura
An sako tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Cif Femi-Kayode daga hannun Hukumar Yaki da yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, bayan shafe kimanin sa’o’i 8 na “kacici-kacici”.
Idan zaku iya tunawa Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta gayyaci tsohon ministan domin yin takaitaccen tambayoyi kan karyar takarda.
Fani-Kayode da wasu mutane 14 na gurfana a gaban kotu bisa zargin almundahanar kudi naira biliyan 3.8 a tsakanin watan Janairu zuwa watan Maris na shekarar 2015.
Kazalika Fani-Kayode dai ya gurfana a gaban kotun da safiyar ranar litinin tare da tsohon ministan kudi da wasu ‘yan tsiraru da ake shari’a kan wasu takardun bogi.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa hukumar EFCC ta gayyaci FFK ofishinta jim kadan bayan da kotu ta yanke hukuncin yin tambayoyi a gareshi.
Sai dai Fani-Kayode, a wani sakon daya wallafa a shafinsa na twitter, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto ya bayyana cewa ba a kama shi ba sabanin rahotannin kafafen yada labarai.
Sannan yace, “An sake gayyata ta zuwa ofishin EFCC a yau. Har yanzu, duk da rahotannin kafofin watsa labaru, ba a kama ni ba amma an gayyace ni. Na isa wurin karfe 11:00 na safe kuma yanzu an sake ni. Godiya ta tabbata ga Allah”.