Gwamnatin jihar Kano ta amince da kafa wani kwamitin da zai binciki hatsarin kwale-kwale da ya afku a kogin Bada zuwa Bagwai a karamar hukumar Bagwai ta jihar.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyanawa manema labarai hakan, bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwar jihar, da ya gudanar a dakin taro na Africa House dake gidan gwamnatin jihar Kano, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 29 ciki har da maza, mata da kananan yara.
Kwamishinan ya ce majalisar ta amince da kafa kwamitin bincike na gaggawa kan hatsarin da sauran su, da baiwa gwamnati shawara kan yadda za a kaucewa afkuwar lamarin nan gaba.
Kwamandan rundunar sojin ruwa na jihar, Kyaftin Muhammad Abubakar Alhassan ne zai jagoranci kwamitin.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da shugaban hukumar kula da manufofi, dabaru, aiwatarwa da tantancewa, Alhaji Rabi’u Sulaiman Bichi; kwamishinonin kasuwanci, sufuri da gidaje, da kuma harkokin addini; wakilin kwamishinan ayyuka da ababen more rayuwa, wakilan kwamishinan kananan hukumomi, hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), Masarautar Bichi, Wakilan Yan jami’an Sirri DSS; da Hukumar Tsaro ta Cibil Defence (NSCDC), yayin da wakili daga ofishin majalisar zartaswa zai yi aiki a matsayin sakataren kwamitin.