By Abbas Yakubu yaura
An ceto jami’in ‘dan sanda reshen Fugar dake jihar Edo, CSP Ibrahim Ishaq, a daren ranar Alhamis.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Edo ne suka ceto DPO din da aka yi garkuwa da shi mako guda daya wuce.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SO Kontongs Bello ya tabbatar da ceto Ishaq, inda yace,“Wannan shine don sanar da jami’an rundunar da ‘yan jarida cewa jami’an rundunar sun ceto CSP Ibrahim Ishaq DPO Fugar daga hannun masu garkuwa da mutane.
Sannan yace yana”Gode wa Allah da jajircewar CP, Philip Ogbadu da suka taimaka wajen kubutar dashi daga hannun masu garkuwa da mutane.”Ya kara da cewa za a yi karin bayani daga baya
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa CSP Ishaq kafin a tura shi Edo shekaru da suka gabata, ya taba rike mukamin DPO a sashin ‘yan sanda na Dakata dake jihar Kano.