By Abbas Yakubu yaura
Kungiyar ‘yan kasuwa, masana’antu, ma’adinai da noma ta Najeriya (Women Wing) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance kalubalen da ke hana shigar mata cikin harkokin sayo kayayyakin gwamnati.
A cewar ta hakan, zai baiwa mata ‘yan kasuwar Najeriya damar bada gudumawar kudi akalla naira biliyan 500bn ga tattalin arzikin kasa a duk shekara.
Kungiyar ta yi nadamar cewa duk da umarnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari mai lamba 003, inda ya umurci dukkan Ma’aikatu, Sashe da Hukumomi (MDAs) na Gwamnatin Tarayya dasu baiwa masana’antun cikin gida fifiko wajen siyan kayayyaki da ayyuka, kashi daya ne kawai ke zuwa kasuwancin mata.
Shugabar kungiyar mata ‘yan kasuwa ta NACCIMA (NAWORG), Hajiya A’isha Abubakar ce ta yi wannan kiran a taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis.
A cewar tsohon Ministan, “Batun daidaito tsakanin jinsi ya samo asali ne a cikin haƙƙin ɗan adam da kuma muhawarar tattalin arziki. Don haka, dole ne a rufe gibin jinsi ya zama wani muhimmin sashi na kowace dabara don samar da dorewar tattalin arziki da al’ummomi.
“Saboda haka, muna ba da shawarwari ta musamman don inganta buƙatun kasuwa da aikin na kasuwancin mata ta hanyar yin amfani da Dokar Shugaban kasa ta 3 da aka buga a cikin shekarar 2017, mai suna, Dokar Zartarwa akan Tallafawa Kan Abun Cikin Gida a Tallafin Jama’a ta Gwamnatin Tarayya.”
A nata jawabin, shugabar kungiyar ‘yan kasuwan mata ta Najeriya Barista Vera Ndanusa, ta bayyana cewa umarnin shugaban kasa mai lamba 003 da 005 ya ba da dama ga mata masu sana’o’i su bunkasa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa “Yayin da a duniya ana kiyasin saye da sayarwa ya kai dala biliyan $5.5, inda Najeriya na kashe dala biliyan 1.1 wajen saye. Wannan yayi daidai da naira biliyan 473bn, iya naira biliyan 4.73bn ne kawai ke shiga kasuwancin mata.
Comments 1