By Abbas Yakubu yaura
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC shiyyar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano yayin da suke yunkurin safarar na’ura mai sarrafa kansa guda 1,144 zuwa wata kasar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wadanda ake zargin sun hada, Abdullahi Usman, Musa Abubakar da Abdulwahid Auwalu, an kama su ne tsakanin 24 ga watan Nuwamba zuwa 1 ga watan Disamba, 2021.
Kazalika da aka kama su, an gano cewa Abubakar dake kan hanyarsa ta zuwa birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, ya boye katin cirar kudi na ATM guda 714, yayin da Usman dake kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya shima yake da katin na cirar kudi na ATM guda 298 a hannunsa.
A wata sanarwa da kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren a ranar Juma’a ya fitar mai taken ‘EFCC ta kama wasu mutane uku da katinan cirar kudi na ATM 1,144 a filin jirgin saman Kano, tace “A daya bangaren kuma, an kama Abdulwahid da katin ATM 132 a lokacin da yake kokarin shiga jirgin kasar Habasha zuwa Istanbul dake Turkiyya.
Kazalika yace “Za a gurfanar da wadanda ake zargin gaban kotu da zarar an kammala bincike.”