By Abbas Yakubu Yaura
Wasu rahotanni na nuni da cewa an kona wani matashi mai matsakaicin shekaru da ake zargi da yin tsafi inda ya mayar da wasu dalibai Doya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin,dai ba a iya tantance sunansa ba, tare da kuma kone shi da safiyar ranar Juma’a.
Wasu fusatattun mazauna garin Ashi, Bodija, da Akobo ne suka kama shi bisa zarginsa da mayar da daliban makarantar sakandaren Bashorun Ojoo guda biyu zuwa doya.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Lamarin ya faru ne a gaban makarantar.sai dai An bayyana cewa an kama mutumin ne a lokacin da aka gano cewa ya mayar da daliban zuwa Doya.
Sai dai Duk kokarin da mazauna garin suka yi na ganin matsafin ya yi nasara kan dawo da daliban zuwa siffarsu ta asali lamarin yaci tura.
A cewar majiyoyin mutumin da suka nemi a sakaya sunansa, an daure shi da igiya tare da yi masa tambayoyi.sai dai Rashin bayar da amsoshin tambayoyin da aka yi masa a zahiri ya sanya mazauna garin suka banka masa wuta.
Daga baya an jefar da ragowar wadanda ake zargin a gaban katangar makarantar.
A cikin wani faifan bidiyo, ya nuna yadda aka daure mutumin da igiya tare da doyar guda biyu da aka ajiye a gabansa. Sai dai ba a sani ba ko da gaske ne ya mayar da daliban zuwa doyar saboda malaman makarantar sun ki cewa komai kan lamarin.
Kazalika duk kokarin da muka yi don jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Adewale Osifeso, shi ma ya ci tura, domin ya kasa amsa wasu kiraye-kirayen da aka yi masa ta wayar salula.