By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasar Gambiya Adama Barrow ya samu dan kwarya kwaryar ja-gora da wuri bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar Asabar, a cewar sakamakon wucin gadi na kananan hukumomin da hukumar zaben kasar ta tantance.
A wani gwajin kwanciyar hankali da ci gaban dimokuradiyya, wannan karamar kasa ta yammacin Afirka na gudanar da zaben farko tun bayan da aka zabi tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh daga mulki a shekara ta 2016, wanda ya kawo karshen mulkin kama karya na tsawon shekaru 22.
Barrow, mai shekaru 56, tsohon jami’in mai gadi ne kuma mai gina kadarori, ya fafata da abokan hamayya biyar, ciki har da tsohon mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ousainou Darboe, mai shekaru 73, wanda ake ganin shi ne babban abokin hamayyarsa.
Sakamakon farko na mazabu hudu daga cikin 53 ya nuna Barrow ne ke kan gaba da kuri’u 14,599 wanda Darboe keda 6,188 inji shugaban hukumar zaben, Alieu Momarr Njai, ya fada a gidan talabijin na kasar da sanyin safiyar Lahadi.
A karkashin tsarin mafi rinjaye, ana sa ran za a sanar da sakamakon wucin gadi a ranar Lahadi tare da fitar da lambobi daga mazabu guda daya a cikin wucin gadi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Gambiya na amfani da wani irin tsarin kada kuri’a na musamman – inda ake jefa duwatsun marmara a cikin gangunan zaben kowane dan takara – domin kaucewa gurbatattun kuri’u a kasar dake da yawan jahilci.
Jammeh wanda ya sha kaye a hannun kawancen ‘yan adawa dake goyon bayan shugaba Barrow mai ci, ya tsere zuwa Equatorial Guinea a shekara ta 2017 bayan ya ki amincewa da shan kaye.
Da sanyin safiyar ranar Asabar Barrow ya kada kuri’arsa a birnin Banjul, ya kuma ce yana da yakinin samun nasara.
Sauran ‘yan takarar sun hada da Essa Mbye Faal, wanda ya taba zama babban lauyan hukumar gaskiya, sulhu da ramuwa ta Gambiya wadda ta yi tarihin cin zarafin mulkin Jammeh, da Mama Kandeh, wacce ta zo na uku a shekarar 2016 kuma Jammeh ke marawa baya.