Rundunar ‘yan sanda na birnin Tarayya a ranar Lahadi, ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare rayukan da dukiyoyin al’umma. Kakakin rundunar ‘yan sanda, DSP Anjuguri Manzahshi ne wanda ya tabbbatar da hakan a wani sanarwa da ya fitar inda ya ce jami’in ‘yan sanda sun samu nasaran ceto wani Malamin jami’ar Baze wanda ‘yan bindiga suka sace a ranar 8 ga watan Satumba, 2019.
Ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike a kan wani bawan Allah da aka saka ce a unguwar Asokoro a ranar Lahadi 14 ga watan Satumba, 2019.