Bayanai daga jami’ar Maiduguri na cewa a daren jiya Lahadi, mayakan Boko Haram sun yi yunkurin kunna kai cikin harabar jami’ar da nufin kaiwa makarantar mummunan hari, amma sun samu tirjiya daga jami’an sojoji.
Wata majiya daga cikin jami’ar ta bayyana cewa a jiyo karar harbin bindiga a kusa da dakin kwanan dalibai mata a yayin gwabzawa tsakanin sojojin Nijeriya da mayakan Boko Haram
Karon battar tsakanin sojoji da ‘yan Boko Haram din ya dauki tsawon awonni biyu ana bata kashi kafin daga baya komai ya tsagaita.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa hukumomi a jami’ar sun tabbatar da cewa harin ne ‘yan Boko Haram suka so kaiwa a kan makarantar, sai da sun samu tirjiya daga sojoji Nijeriya.
Wannan lamari dai ya haddasa firgici mai tsanani a tsakanin daliban makarantar da a yanzu haka ke tsaka da zana jarrabawa.
Wasu dalibai sun yi kokarin tserewa daga sansanin makarantar, amma sai sojoji da sauaran jami’an tsaro suka hana su, inda suka bayyana cewa duk dalibin da ya fita ba za bari ya dawo ba bayan harin.