By Abbas Yakubu Yaura
Lamarin dai mai ban tausayi da ta ajibi ya faru ne a unguwar Jah-Michael dake karamar hukumar Olorunda ta jihar Legas a ranar Asabar.wadanda yaran suke tsakanin shekaru hudu zuwa tara.
Rahotanni sun bayyana cewa yaran sun shaki wani abu ne a cikin wata mota kirar Honda Pilot jeep mai lamba AAA157BD da aka ajiye a harabar daya daga cikin gidan iyayen yaran da suka rasu mai suna Saliat Kazeem.
Saliat ta tsinci gawarwakin ne bayan ta zagaya domin lalubo jikanta.
Saliat wacce ta mallaki gidan da motar tayi fakin dinta a harabar gudan ta inda tana bacci yayinda yaran suka shiga cikin motar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adekunle Ajisebutu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sannan yace, “Yaran takwas an ce sun kulle kansu ne cikin wata mota da aka yasar a lokacin da suke wasa. An tsinto gawarwakinsu an ajiye su a dakin ajiyar gawa na babban asibitin Badagry domin a gudanar da bincike a kan gawarwakinsu domin sanin ainihin musabbabin mutuwar.