Daga: Wakilin Dimukaradiyya Mukhtar Yakubu Kano
Tsohon Shugaban kungiyar kwararru ta masu harkar fim wanda kuma gogagge ne a harkar fim ta duniya Malam Abdulkareem Muhammad ya nuna kalubalen sa ga Masarautar finafinai ta kannywwod da cewar har yanzu basu san ciwon Kan su ba, domin su duk wani taro in ba wanda za a zo a ci abinci kawai a tashi ba, to ba za a gan su a wajen ba.
Sannan ya bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya dangane da bikin Bajekolin finafinan Afirka da aka gudanar a watan daya gabata wanda sai ya zamo ‘Yan fim sun kauracewa wajen.
Ya Kara da cewar “Amma duk wata harkar da zata bumkasa harkar su ba za a gan su a wajen ba, Kuma wannan abin kunya ne, domin duniya ta wuce a ce Jahili shi ne yake jagorantar al’mma”.
Shi dai wannan taron mai taken KILAF AWARD na shekarar 2021 taro ne da a ke shiryawa a duk shekara domin Bajekolin finafinan Africa da gabatar da jawabai domin bunkasa Masarautar fim ta kannywwod da Kuma tallan ta a duniya, wanda Kuma wannan she ne Karo na huda da aka yi a Kano daga ranar 22 ga watan Nuwamba zuwa 23 ga Nuwamba, Amma duk lokacin da a ke shirya taron har a gama da wuya ka samu wasu daga cikin masu harkar fim a Masana’antar Kannywwod sun halarta.
Comments 1