By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa mutum daya ya mutu kana wasu 18 sun jikkata ciki har da wasu jiga-jigan jam’iyyar Ennahdha mai kishin Islama a Tunisiya a wata gobara data tashi a hedikwatarta a jiya Alhamis, kamar yadda hukumomi da ‘yan jam’iyyar suka bayyana.
Ennahdha ya fada a shafin sa na Facebook cewa daya daga cikin masu fafutuka, wanda tsohon mai karbar baki ne da aka haifa a shekarar 1970, ya mutu a cikin tashin gobarar.
Ma’aikatar harkokin cikin gida tace an gano gawar sa a cikin ginin daya kama da wuta.
Kafofin yada labaran Tunisiya sun ambato majiyoyin shari’a na cewa mutumin ya kona kan sa a kasan ginin.
Tsohon firaministan kasar kuma mataimakin shugaban Ennahdha Ali Laaryadh yana kwance a asibiti bayan ya tsallake rijiya da baya daga hawa na biyu na ginin don gujewa gobarar, kamar yadda shugaban kwamitin ba da shawara Abdelkarim Harouni ya bayyana, in ji mambobin jam’iyyar.
Wakilin AFP yace ya ga hayaki na kwarara daga tagogin ginin dake tsakiyar birnin Tunis yayin da jama’a suka taho.
Shugaban jam’iyyar Rached Ghannouchi, kakakin majalisar dokokin Tunisiya da aka dakatar, baya cikin ginin a lokacin da lamarin ya faru in ji jami’in jam’iyyar Mondher Lounisi.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Ennahdha,yace haramtacciyar kungiyar adawa a karkashin mulkin kama-karya na Zine El Abidine Ben Ali, ita ce karfi mafi girma a majalisar dokokin Tunisiya tun bayan juyin juya halin kasar a shekara ta 2011.
Sannan Ta taka rawa a fagen siyasar kasa har sai da shugaba Kais Saied ya kori gwamnati, ya dakatar da majalisar da kuma kwace madafun iko a ranar 25 ga watan Yuli.