Kwamishiniyar harkokin mata da kananan yara ta jihar Zamfara Hajiya Rabi Shinkafi, ta yi murabus daga mukaminta domin sake zama kwamishina a jihar Imo.
“Na ajiye mukamina na kwamishina a jihar Zamfara domin samun damar sake zamana kwamishina a jihar Imo,” Shinkafi ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Gusau ranar Alhamis.
“Ina matukar godiya ga Gwamna Bello Matawalle da uwargidansa Hajiya A’isha Matawalle bisa yadda suka yi min hidima tare da ba ni dama na yi wa Jihar Zamfara hidima a wurare daban-daban.
“Duk rade-radin da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta game da murabus na kwata-kwata karya ce; aiki ne kawai na masu yin barna,” inji ta.
“Ina da cikakkiyar dangantaka da gwamna da matarsa. Ina daukar su a matsayin dangina kuma suna cikin lamurana na tafiyata Imo.
Ta Kuma Kara da cewa, “Dukkanin Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo da Matawalle sun tattauna a matsayin gwamnonin jam’iyyar APC Mai Mulki da kuma abokai, kafin yake wannan shawarar da nayi”