By Abbas Yakubu Yaura
Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 6 ne suka mutu yayin da wasu 6 suka jikkata a wani hatsarin mota daya afku a kauyen Tazame dake karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara a ranar Alhamis.
Hadarin dai ya afku ne a lokacin da wata motar bas Sharon da wadanda abin ya shafa ke ciki ta yi karo da wata motar.
Kwamandan hukumar FRSC reshen jihar Zamfara, Iron Danladi, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Gusau ranar Juma’a cewa motar bas da wadanda abin ya shafa ke tafiya ta nufi Sokoto ne daga Abuja.
Sannan yace direban motar bas din da ba a yiwa rajista ba ya tsallake rijiya da baya a lokacin data bugi motar dake tafe daga wata hanya.
Danladi ya kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin kwararru na Yeriman Bakura dake Gusau domin yi musu magani, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiye gawa dake cikin Asibitin.