By Abbas Yakubu Yaura
Jihar Bauchi ta sake samun karin bullar cutar zazzabin Lassa yayin da mutane 30 daga cikin samfuran da aka dauka ya nuna suna dauke da cutar a cikin kananan hukumomi 6 cikin 20 dake jihar.
Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta Jihar Bauchi (BASPHCDA), Dokta Rilwanu Mohammed ne ya bayyana hakan a Bauchi yayin da yake zantawa da manema labarai.
Dokta Mohammed yace kananan hukumomin da abin ya shafa sun fi yawa a shiyyar Bauchi ta Kudu data tsakiya da suka hada da Bauchi, Bogoro, Ganjuwa, Kirfi, Tafawa Balewa da Toro.
Ya alakanta barkewar cutar a sakamakon girbin amfanin gona da ake ci gaba da yi.
Sannan yace daga watan Janairu zuwa Disambar bana, jihar ta samu jimillar mutane 153 da suka kamu da cutar zazzabin Lassa daga cikin 136 da aka yi wa gwajin tare da tabbatar da mutuwar mutane takwas.
Shugaban yace gwamnatin jihar na daukar dukkan matakan da suka dace na lafiya da kuma rigakafin domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a, inda ya ce nan ba da dadewa ba hukumar za ta samar da karin magunguna da alluran da zasu magance cutar.
Ya shawarci mutane da su kiyaye tsaftar muhallansu domin dakile cigaba da yaduwar cutar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sama da mutane 38 da suka hada da fitattun sarakunan gargajiya ne suka mutu sakamakon zazzabin Lassa a jihar a shekarar 2020 wanda ya kai ga kafa kwamitin da zai shawo kan lamarin.