By Abbas Yakubu Yaura
Wani hatsarin mota ya afku a gadar tafkin Agulu dake kan titin Awka-Ekwulobia a jihar Anambra a yammacin ranar Lahadin data gabata,wanda yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane 11,tare da jikkata wasu mutane hudu a hatsarin.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa hatsarin wanda ake alakanta shi da wuce gona da iri da kuma gudun wuce sa’a, ya hada da motoci uku.
A cewar wani ganau, direban motar kirar Mitsubishi L300 na kan gudu sosai a lokacin da ya wuce, kuma ya yi karo da wata babbar motar da ke tafe ta gaban sa.
Daga baya wata motar safa ta shiga cikin motocin da tuni suka yi karo.
Daga cikin mutane 20 da hatsarin ya rutsa da su, mutane 11 da suka hada da manya maza uku, mace daya da wasu bakwai, sun makale a cikin motar bas din kuma sun kone kurmus.
An ceto fasinjoji biyar ne a cikin motar ta Hiace.
Wadanda suka samu raunuka an garzaya da su asibitin St Joseph yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawa na asibitin.
Kwamandan sashin kiyaye hadurra na jihar Anambra, Mista Adeoye Irelewuyi, ya jajantawa iyalan wadanda suka mutu.
Sannan ya yi kashedi game da wuce gona da iri yayin gudanar da tuki.