By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani direban tankar mai, mai suna Dahiru Aliyu dan shekara 45 a rumbun tara mai na cikin tankar dake Hotoro NNPC.
Tabbatar da hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar a ranar Talata.
Yace “Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin.
A cewar sa“Mun samu kiran gaggawa daga wani Shu’aibu Muhammad da misalin karfe 10.59 na safe, kuma mun aika da tawagar mu zuwa wurin da lamarin ya faru nan take,” inji shi.
Kazalika ya kara da cewa Aliyu ya shiga daya daga cikin ramukan tankar man dauke da jarka da kuma soso dan kwashe ragowar man da ya zube a lokacin zafin cikin wurin yayi masa yawa har takai ga ya daina numfashi ya mutu.
Sannan yace “Motar tana dauke da lamba DKD 411 XF,” in ji Abdullahi.(NAN)