Wata kotun Majistare dake Makurdi a ranar Juma’a ta garkame mutum biyar bisa zarginsu da aikata ayyukan kungiyoyin asiri. Mai Shari’a Ajuma Igama, ba ta karbi rokon wadanda ake zargi ba, bisa hujjar cewa kotun ba ta da wannan damar, inda ta dage shari’ar zuwa ranar 17 ga watan Oktoban 2019.
Mai Shigar da karar Sajen Ato Godwin, ya shaidawa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 28 ga watan Agusta. Dan sandan daga hedikwatar Tse-Agbergba, a karamar hukumar Konshishi ya ce sun samu labarin rikicin da kungiyoyin asirin ke yi a tsakaninsu ta hanyar amfani da muggan makamai.
Wadanda ‘yan sandan suka kama a wurin sun hada da; Akaazua Iortim, Kange Joseph, Terseer Agaagyu, Terkuma Ikyue da Peter Orsugh daga garin Korinya a karamar hukumar Konshisha tare da makamai irin su guduma, adda da kuma sanduna.
Ya tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike dangane da lamarin. Kuma laifinsu ya sabawa sashe na 11 (2) na dokokin garkuwa da jama’a, ayyukan kungiyar asiri, boye mutane, na dokar Binuwe na 2017.