A wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya fitar bisa dogaro da rahoton kungiyar sinimomi ta Nijeriya wato CEAN, sun tabbatar da cewa; ‘yan Nijeriya sun kashe naira Biliyan 1.2 A Sinimu cikin wata biyu. A wani rahoto a farkon watan Yulin ya nuna yadda ‘yan Nijeriya suka kashe naira miliyan 37 da dubu 409 da dari 372 wajen kallon wani fim mai taken ‘Bling Lagosians’ wanda aka saki a watan Yuni ya zama daya daga cikin manyan fina-finai ashirin na Nijeriya da aka fi kallo.
Daya fim din na Kunle Afoloyan mai suna ‘Mokalik’ ya kasance na tara, yayin da ‘Avengers: Endgame’ ya zo na 18, inda aka samu naira 151, 966 a makon.
A mako na biyu, fim mai taken ‘Spiderman: Far from home’ ya zarce fim din ‘Bling Lagosians’ inda ya kasance na farko. Fim din ‘Spiderman’ shi ya ci gaba da rike ragamarsa a mako na uku a matsayin na farko.