Deji Adeyanju ya nuna rashin amincewa akan sha’awar Tinubu na zama Shugaban Ƙasar Najeriya a shekarar 2023 mai zuwa.
A ranar Litinin Tinubu ya shaidawa Manema labaru cewa yayi taro da Shugaban Ƙasa a Villa, inda ya shaida mashi sha’awar shi na tsayawa takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
KARANTA WANNAN LABARIN: NSCDC ta kama wata mai safarar mutane da ƴan mata 6 a Benue
Wannan ƙudiri na tsohon Gwamnan Lagos yana cigaba da haifar da maganganu a tsakanin ƴan Najeriya, inda wasu da dama suke shawartar shi daya banma na ƙasa dashi.
Dayake maida jawabi a ranar Talata, Deji yace Buhari yafi sau Miliyan 10.
A cewar shi, Tinubu zai saida Najeriya ne ga kanshi, kamar yanda ya zargi cewa yayi a Jahar Lagos, yace mutum ne da baida hanyar neman kuɗi sai siyasa.
A lokacin da yake addu’ar cewa wannan fitina kada ta faru a Najeriya, Adeyanju ya bayyana cewar Buhari baya saida Najeriya a gareshi.